Yadda mata 4 saman doki suka kwashe yan kallo a hawan daushe na masarautar Zazzau
Kamar dai yadda aka saba a al'adar malam Bahaushe a kasar Hausa da sallah akan gudanar da bukukuwa da dama ciki hadda hawan dokona da nufin raya al'adun mu da kuma masarautun mu na gargajiya.
To saidai a wannan sallar da ta gabata a masarautar Zazzau al'amarin ya dauki wani sabon salo da wasu mata su hudu suka kwashe yan kallon yayin da suka yo ado saman dawakan su.
KU KARANTA: Rikici tsakanin Ali Nuhu da Rahma Sadau
Legit.ng ta samu dai cewa matan sune Barbara Patricia Zingg, Blessing Mato, Hawwah Gambo da kuma ta karshen su Shamsiyya Zaria. Matan dai sun caba ado irin na kasaita da sarauta da kuma suka riko tutar su ta shahararriyar sarauniyar nan ta Zariya da ake kira Sarauniya Amina.
To sai dai fitowar matan ke da wuya sai kawai kallo ya koma wurin su musamman ganin irin adon da suka caba da kuma yadda ba'a saba ba da hakan.
Ko shakka babu kuma hakan ba karamin karawa bukukuwan sallar armashi yayi ba a garin na zazzau musamman ma kuma ganin yadda aka tunawa jama'a cewa suma fa mata ba'a barsu a baya ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng