Biyafara: Abin da ba na so game da Kanu - In ji dan Ojukwu

Biyafara: Abin da ba na so game da Kanu - In ji dan Ojukwu

- Babban ɗan marigayi Odumegwu Ojukwu, ya ce Nnamdi Kanu ya tafka kuskure

- Ojukwu ya nuna rashin amincewarsa ga kalaman kanu ga mutane wanda ya ce ba daidai ba ne

- Ojukwu ya ce rashin adalcin gwamnati ga mutanen yankin da kuma yin amfani da karfin mulki ya jawo wannan kokarin kafa yankin Biyafara

Cif sylvester Ojukwu, babban ɗan marigayi shugaban ‘yan Biyafara, Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, ya bayyana inda shugaban kungiyar 'yan asalin yankin Biyafara, IPOB, Nnamdi Kanu ya yi kuskure.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Ojukwu ya ce ko da yake Kanu yana da hakkin bayyana ra’ayinsa a kan kafa yankin Biyafara, amma ya nuna rashin amincewarsa ga wasu kalaman kanu ga mutane wanda ya ce ba daidai ba ne.

Da yake jawabi tare da jaridar Sun, Ojukwu ya lura cewa sabuntawa ga kafa yankin Biyafara ya na da nasaba da rashin adalci ga mutanen yankin da kuma yin amfani da karfin mulki.

Biyafara: Abin da ba na so game da Kanu - In ji dan Ojukwu
Cif sylvester Ojukwu, babban ɗan marigayi shugaban ‘yan Biyafara, Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu

Da aka tambaye shi ko Kanu ya cika gurbin da mahaifinsa ya bari a baya, tsohon jami'in ‘yan sandan ya ce, "Kamar yadda na fada maka, ba zan iya shiga wannan ba, kuma ba zan iya cewa mahaifina ya kasa horar da wanda zai gaji shi ba”.

KU KARANTA: Biafra: Abin da zai faru da Najeriya idan an kashe ɗana ko sake kame shi – in ji mahaifin Nnamdi Kanu

"A wasu lokuta, mahaifina ya na cewa da yaushe ba shi da magaji. Ya ce yana da kyakkyawar shiri amma yana neman mai maye gurbinsa".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng