Rikcin Kasar Burma: An Samu Tsagaita Wuta a Kan Kabilar Musulmi Ta Rohingya

Rikcin Kasar Burma: An Samu Tsagaita Wuta a Kan Kabilar Musulmi Ta Rohingya

- Wata kungiya da ake kira ARSA ta bayyana matakin tsagaita wuta daga bangaren ta

- Kungiyar ta dauki matakin ne domin bawa kungiyar agaji ta "Red Cross" damar aikin ceto

- Sama da mutum 300,000 ne 'yan kabilar ta Rohingya ke zaman gudun hijira a kasar Bangladesh

Wata kungiya da ake kira ARSA, mai rajin kare kabilar Rohingya ta musulmi da ke kasar Burma, ta bayyana matakin tsagaita wuta daga bangaren ta domin ba wa kungiyoyin agaji na kasashen ketare damar bayar da gudunmawa ga wadan da rikici ya illata.

Rikcin Kasar Burma: An Samu Tsagaita Wuta a Kan Kabilar Musumi Ta Rohingya
Kabilar Musulmi ta Rohingya ke tserewa zuwa Bangladesh

Kungiyar ta dauki wannan matakin ne bayan da hukumar agaji ta "Red Cross" ta kara adadin jami'anta domin bayar da taimakon gaggawa ga jama'ar musulmi da barkewar rikicin ya tagayyara a yankin arewa maso yammacin kasar ta Burma bayan yamutsewar al'amura.

DUBA WANNAN: Cin zarafin bil-adama: Rahoto kan kisan gillar da ake yi wa musulmi a hannun limaman addinin Buddha a kasar Burma

Sama da mutum 300,000 ne 'yan kabilar ta Rohingya ke zaman gudun hijira a makobciyar kasar Bangladesh yayin da fiye da wasu 30,00 su ka rasa muhallin su tun bayan yakin da sojin kasar suka kaddamar a kan 'yan tawayen kabilar ta Rohingya wato "ARSA" wadda ta yi ikirarin kaiwa cibiyoyin 'yan sandan kasar 30 hare-hare a cikin watan Agustan da ya gabata.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng