Kishi ko hauka: Karanta yadda wata mata ta kashe jaririn kishiyar ta a jihar nan ta Arewa

Kishi ko hauka: Karanta yadda wata mata ta kashe jaririn kishiyar ta a jihar nan ta Arewa

Mai magana da yawu ko kuma kakakin hukumar rundunar yansandan jihar Bauchi dake a arewa maso gabashin Najeriya mai suna DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da labarin da a halin yanzu yake ci gaba da yaduwa na kashe jaririn da wata mata ta yi na kisiyar ta.

DSP Datti yayi wannan karin hasken ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jihar inda a cewarsa ranar 19 ga watan da ya gabata ne a wani kauye dake cikin karamar hukumar Alkaleri ne a gidan wani Abdullahi ita matar ta shiga dakin uwargidan ta dauki jaririnta ta bashi guba.

Kishi ko hauka: Karanta yadda wata mata ta kashe jaririn kishiyar ta a jihar nan ta Arewa
Kishi ko hauka: Karanta yadda wata mata ta kashe jaririn kishiyar ta a jihar nan ta Arewa

KU KARANTA: An cirewa jajiri hakora 7 ringis

Legit.ng dai ta samu daga majiyar ta mu cewa daga baya dai an kai yaron gidan magani dake kauyan amma rai yayi halinsa. DSP Datti ya kuma kara da cewa ita matar da ta aikata danyen, aikin an kamata tana hannunsu.

Haka ma dai kamar yadda ya shaidawa majiyar mu, matar ta amsa laifinta da kanta ba tare da wani matsi ba kuma yanzu yansandan na shirin gurfanar da ita gaban kotu domin a yi mata hukumci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng