Ramuwar gayya: Makiyaya sun kashe mutane 20 a ƙauyen jihar Filato
Kimanin mutane 20 ne suka rayukansu sakamakon wani hari da ake zargin Fulani makiyaya da kaiwa kauyen Ancha dake gefen garin Jos.
Shafin BBC Hausa ta ruwaito mutane da dama sun jikkata sakamakon harin, wanda ya faru a daren Alhamis 7 ga watan Satumba a kauyen na Ancha dake garin Bassa.
KU KARANTA: Soyayya ta koma ƙiyayya: Wani Ango ya aika da Amaryarsa zuwa barzahu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito jama’an garin suna zargin makiyaya Fulani da aikata musu wannan mummunan ta’asa sakamakon ramuwar gayya bisa kisan wani dan uwansu da aka bafulatani da aka a makon data gabata.
Idan ba’a manta ba an dauki lokaci mai tsawo ba’a samu tashin tashina ba a jihar Filato tun bayan da jami’an tsaro suka zage kaimi, sa’annan aka samu hadin gwiwar sarakunan gargajiya wajen shawo kan al’ummansu akan su rungumi zaman lafiya.
Jihar Filato na cikin jihohin dake tsakiyar Arewacin Najeriya ne, kuma tana yawan jama’a mabiya addinin Kirista sosai dake cudanya da Musulmai Hausawa da Fulani.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng