Soyayya ta koma ƙiyayya: Wani Ango ya aika da Amaryarsa zuwa barzahu

Soyayya ta koma ƙiyayya: Wani Ango ya aika da Amaryarsa zuwa barzahu

Rundunar Yansandan Najeriya reshen jihar Bayelsa tayi caraf da wani mutumi mai suna Stephen Akpata sakamakon zarginsa da take yin a hallaka sabuwar Amaryarsa Onyinye Eze, inji rahoton jaridar Premium Times.

Stephen Akpata wanda ma’aikaci ne a kamfanin sadarwa na Globacom ya hallaka Amaryar tasa ne a ranar 16 ga watan Agusta a gidansu, inda yayi amfani da wayan dutsen guga ya shake mata wuya har sai tace ga garinku nan, sa’annan ya caccaka mata wuka.

KU KARANTA: Rikicin hawan Daushe a Kano: Jiga jigan Kwankwasawa sun miƙa takardar koke ga hukumar Yansanda

Kwamishinan Yansandan jihar Bayelsa Asuquo Amba yace sun samu labarin mutuwar Amarya Onyinye ne bayan da abokan aikinta suka kawo kara cewa kwana biyu basu ganta a wajen aiki ba, don haka suka je su duba ta a gida, amma da isarsu sai suka tarar da kofar dakin ta a kulle, kuma talabijin na aiki.

Soyayya ta koma ƙiyayya: Wani Ango ya aika da Amaryarsa zuwa barzahu
Angon da Amaryarsa

Don haka sai suka garzaya ofishin Yansanda inda suka taho da jami’an Yansanda, wadanda suka balla kofar d akarfin tsiya, yin hakan keda wuya, sai suka tsinci gawar Oyinye kwance cikin jini.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kwamshinan Yansandan yana fadin ba tare da da bata lokaci ba suka shiga farautar mijin Oyinye, inda bayan sati biyu suka samu nasarar kama shi a garin Legas. Kwamishinan yace abubuwan da suka gani a dakin da aka kashe matar sun hada da gajeren wando, takalmin kambas, dutsen guga, rigar sanyi, wuka, yar ciki, wayar NOKIA da agogo dukkaninsu dauke da jini a jikinsu.

Kwamishinan ya cigaba da fadin cewa da fari mutumin ya gudu zuwa kasar Ghana, amma daga bisani ya dawo Najeriya, inda suka samu damar cafke shi, daga karshe Kwamishinan yace zasu gurfanar da mutumin gaba kotu da zarar sun kammala bincike.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng