Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Dawajewa: Wannan rubutu dai ra'ayin marubuci ne, ba lallai ra'ayin jaridar Legit.ng ko sauran ma'aikatanta ba, fata na kawai sakon dai ya isa gare shi.

READ THIS IN ENGLISH: An Atheist's response to the Boko Haram leader's video

Kungiyar Boko Haram ta jima tana zub da jinin mutane, da yada fasadi a doron kasa, bisa burinsu na korar tsarin sekulanci da dimokuradiyya, korar ilimin boko da zamananci, domin kawo nasu tsarin na shari'a da dokoki kamar yadda addininsu ya tanada. Sun kuma dawo da baytar da dan-adam kamar yadda aka yi a zamunnan da. Wannan martani ne ga limaminsu Malam Abubakar Muhammad Asshakawy.

Ina kishingide a otal dina a Kano, na shigo bikin babbar sallah, ina bincike don rubutu kan cin zarafi da kisan gilla da limaman addinin Buddha ke yi wa musulmai a kasar Burma, inda suke yi musu kisan kare dangi, da sunan 'addininsu na zaman lafiya', sai tashar labarai ta sako faifan bidiyonka, inda kake nuna wa sojin Najeriya gazawarsu da cimmaka a kwanaki 40 da suka diba domin kamo ka da rai ko babu rai.

Bayananka sun tabbatar min lamarinka ashe harda jahilci, wannan shi yasa nace bari na yi maka wasika, in wayar maka da kai, ko ka tuba ka dena kashe mutane a banza. Barnar da kayi wa al'ummarka da Najeriya ta isa haka, kuma a fata na ko da kai baza ka shiryu ba, mabiyanka zasu karanta, su karu, su kuma farka, kamar yadda muka yi sa'ar warkar da wasunku suka gane zubda jini ba shine hanyar rayuwa ba, lokutan da sunkan yo waya domin tambaya. (+2348032880989 sakon text kawai).

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

A cikin bayananka, ka soki ilimin boko, da tsarin sakulanci, kace kai addininka ka dogara da shi. Ka kasa ganewa, cewa addininka, bai kawo mana bindigar da ka dogara da ita ba, ko da allurar malariya, bai kawo mana agogon dake hannunka ba, bai kawo mana fasahar bidiyo da kuke nada ba, balle motocin da kuke hawa domin zuwa sata, fashi da cin zalin kauyawa, da sunan jihadi.

KARANTA KUMA: Ya kai karar matarsa saboda bata iya karanta Qur'ani ba

Ban dauke ka jarumi ba, in dai sai wadanda basu da makamai ne abokan fadanku. Ku makala wa karamar yarinya bam kuce ta karanta surori daga littafan larabawa, abin takaici! Naso a ce gwamnati ta rarrabawa kauyawan nan makamai su kare kansu, muga ko za'a dinga jin tsoron zuwanku garuruwa ku kwashe wa mutane abinci da iyalai, zamanin Qurayza da Hunayn da Khaybar ya wuce.

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Da zaka fahimci cewa duk abin da kake yi aikin banza ne, babu riba ko ta sisin kwabo, da ka ajje makamanka, ka yi hijira, kaje Saudiyya ka rayu, ka je can kasar wadanda suka aiko mana wannan addini naka mai son rarraba kan mutane, mai koyawa musulmi kashe musulmi wai don dan shi'a ne, ko wai don dan darika ne, ko wai don shi ya zabi dimokuradiyya bayyi rayuwa karkashin khilafa ba. Da ina da hanya sai na tilasta Saudiyya da Iran biya diyyar dukkan barnar da akidunsu suka yi wa 'ya'yanmu, da aiken su na littafan zafafa ra'ayi, na tatsuniyoyin larabawa.

Kaje can, zaka sami shari'ar da kake nema a can, domin mu a nan, wadanda muka ajje addinai muka gano ilhadi maimakon jihadi, da mutumtaka maimakon zabalbalar tsana, wato atheism da humanism, sarai muna sane da kiranka, kuma muna sane da tarihin daular Islama ta da, har ya zuwa ta Usman danFodiyo, amma muka gwammace muyi dimokuradiyya da ilimin boko da sakulanci, babu kuma yadda zaka yi. Baza muyi mubayi'a ga khalifa ko imami ba, mai neman hakan ya tafi Iran ko Iraqi, wannan tsarin ya tsufa, tunani ne na mutan da, asadirul awwalina ne da babu adalci ko hankali a cikinsa.

DUBA WANNAN: Kasashe 25 da ke gaba-gaba wajen karfin soji a duniya

A duk wani tsari da ya yarda a sayar da dan-adam, don bautarwa, wanda addinai duka suka bari aka ci gaba da yi, har sai da su Abraham Lincoln suka waye suka haramta, tsari na a far wa alkarya domin basu bi wani addini ko akida ko al'ada ba, akwai zalunci a cikinsa. Gata ne da ka kasa ganewa, tumbuke daular da turawa suka yi, suka hana aje dazukan Fulato da Kaduna a kamo bayi 'arna' na kan dutse a sayar a Sakkwato da Kano, gata ne Luggard yayi wa dan-adam, shi wannan din da ka tsana kake tsine wa. Ka karanta littafin Tafawa Balewa na Shehu Umar, yayi bayani dalla-dalla yadda bautarwar take a zamanin da a farkon littafin.

Ina sane kuma da hadisai da ayoyi da ka dogara da su, wai 'inni umirtu an uqatilan nasa, hatta yash-hadu an laa-ilaha illal-lahu...', cewar wai 'an umarce ni da in yaki mutane, har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah....' wannan duk mun dena amfani dasu, domin babu adalci a ce sai mutum ya bi wani addini dole. ko aya ta ci karo da wannan, duk dai a addini daya. Abin dariya.

Ilimin bokon da ka tsana, shi ya wayar mana da kai muka gane babu Allah, babu Alloli, babu gumaka, babu tsumurburori, babu aljannu, babu mala'iku, babu iskokai, babu aljannu, babu ifritu, babu lahira, babu wuta, babu aljanna, babu hisabi, babu rai, babu siratsi, babu ghaybu, kamar yadda ka zarga, ka chanka daidai. Mu duka sabulowa muka yi daga halittu na baya, kuma zamu mutu mu koma kasa kamar ba'a yi mu ba Ka binciki meye Evolution da Biochemical processes, zaka kara wayewa. Wannan shine ilimin boko, masu kunar bakin wake su gane asarar rayuwarsu kawai zasu yi, babu wani Allah da zai musu sakayya da wasu mata, ko sau nawa zasu biya 'bal-ahya'un inda rabbihim yurzakun'.

ZAKU SO WANNAN: Shugaba Buhari ne zai lashe zaben 2019, inji fadar shugaban kasa

Da kasan cewa dukkan addinai tatsuniya ne, da baka zafafa cikin imaninka da hikayoyin larabawa ba, da ka fahimci ilimin kimiyya ko da yaya ne, ba almajirta da aka kai ka ba, da ka san cewa zazzafan imani komai girmansa baya tabbatar da gaibu. Misali, ko da duk duniya zata yi kakkarfan imani cewa akwai doki mai tashi mai suna buraqah, imani ne kawai, babu doki mai fiffike, kamar yadda babu gunki mai fuskar giwa a zahiri, wadda indiyawa biliyan guda ke bautawa, duk da duk sunyi imani mai karfi cewa akwai ta.

Ilimin boko shi ya karyata batunka cewa wai duniya a baje take, duniya a dunkule take, kamar kwai, kuma ruwan sama tururin teku ne baka canka dai-dai ba, in kana so ka gane ka dubi tururin da ke dukan murfin tukunya sannan ya koma cikin girki. Ina kana so ka gane yadda duniya take ka nemo yaranka su sauko maka da google-earth ta waya, zaka ga yadda duniya take daga sama, zaka ma ga sambisa har inda kake kwance daga sama, ana iya zukowa. Naso ka dandana dadin boko.

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Karin hujja, ka kalli duk abubuwa da ke sama, rana, wata, da sauran ranoni da ke nesa da duniya, wadanda ake kira taurari, dukkaninsu a dunkule suke kamar kwallo, duniyar ma haka take, ilimi ko iya na sakandare ya isa ka san haka, shi yasa nake takaicin almajirci, domin suma haka suke zaune, miliyoyin yara, basu sami damar jin ilimin boko ba, sai hardace zantukan larabawa da ke koya wa mutanenmu kisan kai da tsanar juna, tsoro na kar nan gaba ku karu da yawan wadannan yaran, fata na ace mai hankali a shugabanninmu zai iya hangowa... Ni kam tun a 2000 na hango faruwar ku Boko Haram lokacin da Yeriman Bakura ya dawo da Shari'a arewa.

Godiya daya kawai da zanyi maka, shine, ko da na gane babu Allah lokacin ina jami'a, na ja baki na nayi shiru, saboda a lokacin ina tsoron kisan da za'a yi min in aka gane nayi ridda, kwatsam sai kuka fidda bidiyo a 2013, kuna yanka wata kiristar yarinya, tana cewa 'ni ba DSS bace...' amma kuka kashe ta. Wannan takaici ya sa ni kuka, da bakin ciki, wai a kasarmu ake wannan bala'in, da yarenmu da addinin da muka dauka namu ne. Yanzu kam, na daina tsoro, ban damu na mutu kan gaskiya ta ba, kuma babu mai iya taba ni, a cikin shiri nake tsaf.

Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram
Budaddiyar Wasika zuwa ga Abubakar Shekau, daga Mubarak Bala: Martani na sakon Bidiyon Boko Haram

Daga baya nace bazan yi shiru ba, tunda dai ashe addinin karya ne, kuma ya fara kashe mutane a gida, na gaya ma kaina wallahi sai na gaya wa duniya, musamman arewar Najeriya, sai dai nima in mutu garin fadin hakan! Daga ffarawa ta, sai gashi ashe mutane da yawa sun gane, kawai shiru ake yi ashe, ko domin shi ne tsarin da ke tafiyar da talakawa, oho. Addinai dai guba ne, sun dora mutane bisa magagi, magagin imani, bisa karya da tsoratarwa, makarin gubar nan shine ilimin boko, da sakulanci, kana sha, zaka gani babu Allah, sai ka zaba, ko dai ka yi son kai, ko kayi son jama'a da rahama.

Ina godiya da ka wayar min da kai cewa ba munafunci, addinin nan dai ba addini ne na zaman lafiya ba, addini ne da ake son yin jihadi, kuma tun kafuwarsa ake zub da jinin jama'a ana kabbara, sahabbai sunyi, su danFodiyo sunyi, su Maitatsine sunyi, kuma gashi kuna kai. Idan aka ci gaba da bin addinin kuma. jinane zasu ci gaba da zuba, musamman a arewa. Ni kam, na zabi zaman lafiya, son bil-adama, kyautata zumunci, yada ilimi cikin raha, kirki, kyauta, girmama masu kirki, tsayawa gaskiya, da jajircewa kan kare maras karfi, da duk iya nawa karfina, ko da kuwa zan rasa komai a kan hakan. Hakan na zaba, hakan shine cikakken 'yanci, 'yanci da ka tsana.

GA FASSARAR WANNAN RUBUTU DA TURANCI (This article in English): An Atheists rebuttal to the latest Shekau video, mocking education, democracy and secularism

Wannan bayani nawa ba lallai ya shiryar da kai ba, domin ko sanda ka tsine min a wani faifan bidiyonka a 2014, ka riga ka fahimci akida ta, da inda na dosa. Sa'a daya dai, itace mabiyanka suna ta kara wayewa, suna jin sabon ilimi, suna tuba, suna dawowa gari suyi rayuwa mai kyau, watakil in suka sake jin wannan sakon, su kara baro ka su gudo. A karshe, zasu baro ka kai kadai da kamammun matan mutane da ka sato, sai dai bamu sani ba ko imanin da suka yi da kai da gaske ne? Ko kuwa tarihi ne zai maimaita kansa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng