Hukumar yan sanda za ta fara dauki ma'aikata 31,000 a kowace shekara
- Idris ya kaddamar da sabuwar hedkwatar yansanda a Nasarawa
- Jama'a su taimaka wa yansanda da rahotanni masu amfani
- Matakin daukan ma'aikata kowace shekara zai magance matsalar karancin yansanda a Najeriya
Sifeto janar na yan sandan, Ibrahim Idris, ya ce rundunar za ta dauki ma'aikata 31,000 a kowace shekara.
A jawabin da Idris yayi yace, yin haka zai magance matsalar karanci ma’aikatan yansanda a kasar.
Shugaban yansandar ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a lokacin da yaje kaddamar da sabuwar hedkwatar yansada a Lafia jihar Nasarawa.
KU KARANTA : El-Rufai ya mai da martani akan yada jitajitan ‘canza’ mataimakin sa
“Bayan karanci ma’aikata, za mu yi kokarin samar da isassun makamai ga hukumomin mu dake fadin kasar nan,”Inji shi
Idris ya yi kira ga al’ummar Najeriya, da su taimaka wa' yan sanda ta hanyar kai musu rahotanni masu amfani dan gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng