Nayi sana'ar yin ciyawa sadda ina yaro karami - Gwamna Masari

Nayi sana'ar yin ciyawa sadda ina yaro karami - Gwamna Masari

Tsohon kakalin majalisar tarayyar Najeriya daga shekara ta 2003 zuwa 2007 kuma Gwamnan jihar Katsina dake a arewacin Najeriya RT Honarable Alhaji Aminu Bello Masari ya bayyana cewa sadda yana yaro karami dan makarantar Firamare yayi sana'ar saida ciyawa don ya ci da kansa.

Gwamnan ya yi wannan ikirarin ne a yayin wani bukin kaddamar da dalibai watau Matriculation a turance na makarantar fasaha da kuma koyon harkokin gudanarwa watau Katsina State Institute of Technology and Management a turance.

Nayi sana'ar yin ciyawa sadda ina yaro karami - Gwamna Masari
Nayi sana'ar yin ciyawa sadda ina yaro karami - Gwamna Masari

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta gano wani muhimmin ma'adani a arewa

Legit.ng ta samu cewa gwamnan ya fadi hakanne yayin da yake yin jawabi ga daliban da aka kaddamar na makarantar su 136. Gwamnan a cikin bayanin nasa ya bukaci daliban da su kama yin sana'a a lokacin hutu komin kankantar ta don kuwa itace rufin asirin mutum kawai.

A cewar sa idan mutum ya samu hutu daga makaranta ya kamata ya fara yin wata sana'ar komin kankantar ta ba tare da sa girman kai ba. Gwaman yace: "Kuna iya fara tallar aya ko dabino da dai sauran su da jarin da bai wuce na Naira N1,000."

A cewar Gwaman yin sana'a domin samun na kai yafi kima da daraja akan yawon maula da rokon masu yahhu da shuni.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng