Sunayen wasu kamfanoni mallakar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya lissafo sunayen wadansu daga cikin kamfanonin da ya mallaka a wata tattaunawa a shafin dandalin sada zumunta na 'twitter'.
Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne a yayin mayar da martani akan tuhumar da ake yi ma sa na cewar shi ke da mallakin kamfanin injinan samar da wutar lantarki na Mikano.
An tuhumi tsohon shugaban kasar da cewar idan ya hau mulkin kasar nan a zaben 2019, 'yan Najeriya za su shiga cikin kangin rashin wutar lantarki domin kamfanin na sa na Mikano ya samu shiga a kasuwannin kasar nan.
Daya daga cikin wadanda suka tattauna da tsohon shugaban kasar mai amfani da sunan @adewoleade, ta tuhumci Atiku da mallakin kamfanonin sanadiyar kudade kasa da ya wawushe tun daga shekarar 1999 zuwa 2007 a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa.

Wata kuma mai sunan Sobajo @najash_sani ta bayyana ma sa cewar, shine yake da mallakin sadarwa na Gotel wanda aka kafa tun a shekarar 2008, jami'ar A.U.N da kamfanin Faro duk an kafa su ne a shekarar 2004.
Alhaji Atiku ya lissafo sunayen wadansu daga cikin kafanonin na sa kamar haka;
1. NICOTES (wanda yanzu ya koma da sunan INTELS) shekarar kafuwa 1989.
2. PRODECO, shekarar kafuwa 1996.
3. Gonarsa, shekarar kafuwa 1982 da kuma
4. Makarantun ABTI, wanda aka kafa su tun shekarar 1992.
KU KARANTA: Kashin kadangare ya raba wata budurwa da yatsan ta guda a Jigawa
A yayin tattaunawa, ya bayyana cewa, "wannan alakantani da kamfanin Mikano da kuke yi ba gaskiya ba ne, ina da manyan kamfanoni wanda sanannu ne a kasar nan, saboda haka me zai sanya na ce kamfanin Mikano ba nawa bane."
Ya ce"Ga kamfanin Intels wanda shine mafi girma a cikin kamfanonin samar da man fetur na kasar nan a shekarar 1994."
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng