Kashin kadangare ya raba wata budurwa da yatsan ta guda a Jigawa
A can jihar Jigawa kuma, wata daliba 'yar aji uku a makarantar sakandire Safiya Abbas Ahmed, ta rasa yatsanta guda bayan da shafa kashin kadangare a wani rauni na yankan wuka da ta samu a yatsan.
Rahotanni daga makarantar sun bayyana cewa, ministirin ilimi ta shiga ta yi ruwa da tsaki akan wannan al'amari, bayan da Safiya ta dauki shawarar wata mata mai tsaron su akan cewar ta mulka kashin kadangare a raunin na don a cewar ta wannan mata magani ne gargajiya.
Safiya mai shekaru 15 da haihuwa kuma dalibar makarantar Government Girls Junior Secondary School ta karamar hukumar Miga a jihar ta Jigawa, ta kasance cikin wani mawuyacin hali na radadin raunin dake yatsan ta, duba da gazawa na mika lamarin da ta ke ciki ga shugabannin makarantar, sanadiyar jan kunne da shugaba ta makarantar ta yi akan kawo mata wani korafi bayan lokaci na daukan darussa a makarantar ya kare.
Karaji da koke-koke na Safiya cikin dare, ya sanya wanna mata mai tsaron su ta bata shawarar mulka kashin kadangare ko za ta dan samu saukin ciwon, wanda cikin rashin sani ashe wajen neman gira za a rasa idanu domin kuwa nan da nan yatsan ya kumbure cikin kankanin lokaci.
Duk da irin tabarbarewa da ciwon Safiya ya yi ba ta samu kulawa ba, sanadiyar rashin asibiti a makarantar kuma ga shi karshen mako ne domin kuwa shugabar makarantar ta yi tafiyar ta zuwa jihar Kano.
Duba da rashin kulawa da Safiya ta gani, shine ta roki alfarmar wani malaminsu akan ya kira mahaifinta ta wayar sadarwa domin ya zo ya mika ta asibiti domin neman lafiyarta.
Safiya ko taron ranar Litinin da aka saba gudanarwa a makarantu ba ta iya halarta ba, sai kawai ta yi zaman ta cikin aji tana rusa kuka, wanda hakan ya janyo hankalin shugabar makarantar, inda ta ga halin da wannan yarinya ke ciki.
Cikin gaggawa mahaifinta Mallam Abbas Ahmed ya zo har makaranta, inda ya garzaya da ita babban asibiti dake garin Jahun, kuma suka bayyana musu cewa ai wannan yatsa ya harbu sanadiyar wannan kashi na kadangare.
A wannan lokaci ne hankalin Mallam Abbas ya tashi, wanda hakan ya sanya ya kai 'yar ta sa wani asibitin Rasheed Sekoni a garin Dutse, kuma suka sanar da shi daidai da abinda wancan asibiti na farko akan cewar sai dai a gutsure wannan yatsa.
KU KARANTA: Ta leko ta koma: Shugaban rundunar hadin gwiwa da wasu dakaru sun tsallake rijiya da baya
A jawabin Safiya, ta bayyanawa manema labari cewar ta samu wannan rauni ne sanadiyar yankan albasa domin hada kayan shan ruwa na wani azumin nafila da ta gudanar, kuma tace ba wani babban rauni ba ne sai dai kurum ya zamto raina kama kaga gayya.
Mahaifan Safiya sun tayar da kayar baya akan sai an biwa 'yar su hakkin ta, domin sun tabbatar da cewar rashin kulawa ya janyo faruwar wannan abu duk da sanin cewa tsautsayi ba ya wuce ranar sa.
Kwamishinan Ilimi ta jihar Jigawa Rabi Ishaq, ta bayar da umarnin bincikar wannan makaranta da kuma shugaba ta wannan makaranta domin daukan matakai akan irin rashin kulawar su.
Domin shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng