Sarkin Kano ya ziyarci sabon asibitin Giginyu da gwamnatin jihar ta kammala kwanan nan (Hotuna)
- An kammala babban asibitin Giginyu wanda gwamnatin jihar Kano ta gina kwanan nan
- Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude asibitin
- Sarki Sanusi da shugabannin gundumarsa sun ziyarci babban asibitin Giginyu
Mai martaba sarkin Kano Mal. Muhammadu Sanusi II da shugabannin gundumarsa sun amsa kiran gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje don ziyarar babban asibitin Giginyu wanda gwamnatin jihar ta kammala kwanan nan, daga bisani ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bude asibitin.
Legit.ng ta tattaro cewa, sarkin ya kasance tare da kwamishinan lafiya, Dokta Kabir Ibrahim da kuma babban sakataren harkokin kula da asibitin, Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa, yayin da suka zagaya da tawagar sarkin don ganin wa idanunsu.
Sarki Sanusi ya taya gwamnatin jihar Kano a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje murna a kan babban aikin.
KU KARANTA: Hotunan yakin neman zaben shugabancin kasa na Kwankwaso ya cike Jigawa kafin 2019
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng