Ba maraya sai rago: Kalli wata ýa-mace dake aske kawunan maza (Hotuna)

Ba maraya sai rago: Kalli wata ýa-mace dake aske kawunan maza (Hotuna)

Wata mata mai suna Kehinde Onaopemipo yar asalin jihar Osun ta bayyana yadda tsananin ganin ta zauna da kafafunta ya shigar da ita sana’ar aski, inda har maza ta keyi ma aski.

Matar ta bayyana cewa ta fara koyon aski ne sakamakon talauci da yayi mata katutu kamar yadda ta bada labarinta a shafin Abuja Humans na Facebook, hakan ya sanya na baiwa iyayen zabi biyu, kodai in zama bakanike ko kuma mai aski.

KU KARANTA: Boyi boyin sun taƙaita Maigidansu, sun sace masa naira miliyan 11

Nayi fama da kalubale iri iri a kokari na na zama kwararriyar mai aski, inda tace har faifan CD suna siyarwa a shagon nasu, sa’annan tayi fama da maza masu nemanta da alfasha, amma mai gidanta a shagon ya bata kariyar data dace.

Ba maraya sai rago: Kalli wata ýa-mace dake aske kawunan maza (Hotuna)
Kalli wata ýa-mace dake aske kawunan maza

Kehinde tace ta taba shan mari a wajen wani dan tasha wanda ta lalata ma gashi garin yi masa aski,kamar yadda ta shaida ma majiyar Legit.ng. sa’annan tace ta yi kananan aikace aikace irin su sharan shago, da zuwa aike, da kuma wanke babur din Ogan ta.

Amma daga karshe Kehinde tace duk wadannan kalubale da tayi fama dasu basu hana ta cigaba da kokarin cika burinta ba, inda tace tayi hakuri, ta jure, daga karshe kuma taci moriyar hakurin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng