Shugaban Boko Haram Shekau yana tsoron kamu – Rundunar Sojojin Najeriya
- Shekau yana cikin tsoro
- Ilar da sojoji suka yiwa kungiyan Boko-haram yasa suka fitar da sabuwar bidiyo
- Muna kira da shekau da ya fitar da sabuwar bidiyo da zai nunu kwamandojin da ya karyata ankashe a raye
Rundunar soji Najeriya ta ce shuagaban kungiyan Boko Haram Abubakar Shekau yana cikin tsoro.
Shekau, a wani sabon bidiyon da ya fitar ya karyata sojojin Najeriya akan kashe manyan kwamandojin kungiyar su.
Da yake jawabi, mai Magana da yawun rundunar, Brigadier General Sani Usman, a ranar Laraba, ya ce shugaban Boko Haram yana cikin damuwa saboda irin ilar da sojoji suka kai wa yan kungiyan.
A Sanarwar da yayi yace: "Rundunar sojan Najeriya ta lura da cewa illar da suka wa kungiyan, shiyasa 'yan ta'addan Boko Haram su ka sake fito da wata sabuwar bidiyo a jiya, inda suka tayi wa al’umman Najeriya barazana, kuma suka karyata rahotan mika wuya da wasu' yan kungiyan suka yi, da kashe msu manyan kwamandojin su 5 da aka yi.
KU KARANTA : Yan fashi da makami sun fafata da yansanda a Katsina
“Sojoji sun samu nasarar kashe mataimakan shugaban kungiyan guda biyu, Afdu Kawuri da Abubakar Banishek, a haren da suka kai a ranar Sallah 1 ga watan Satumba 2017."
“An kara kashe Ba’Abba Ibrahim da wasu kwamandoji biyu da suka mutu ta dalilin raunukan da suka ji a lokacin da sojoji suka kai musu kantan bauna a karamar hukumar Magumeri a jiahr Borno."
“Muna kira dashugaban kungiyan Boko haram da ya fitar da sabuwar bidiyo da zai nuna mana kwamandoji 5 din da ya karyata an kashe su a raye."
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng