Zan kashe duk wanda ya taɓa matata – Inji wani babban Fasto
- Fasto Enoch Adeboye ya yi gargadi cewa zai kashe duk wanda ya taɓa matarsa
- Adeboye ya ce idan wani ya taba masa mata zai yi magana da Allah kuma mai shi ba zai farka daga barci ba
- Faston ya shawarci ma'aurata su kasance a shirye su sadaukar da ransu ga mai dakinsu
Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God , RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya yi gargadi cewa zai kashe duk wanda ya taɓa matarsa, Fasto (Misis) Foluke Adeboye.
Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar, Fasto Adeboye, wanda aka fi kira da "daddy G.O" ya ce mutane na da ‘yanci su yi masa mari, ko a zarge shi ko kuma karya a kan shi, ya ce bai damu ba, amma duk wanda ya yi haka ga matarsa, zai kashe mutumin.
“Ina so duniya ta sani. Za su ce idan na yi kisa, za a kama ni, a ɗaure ni, to, idan na kashe mutun da makami ko da bindiga ke nan”, inji Adeboye.
Adeboye ya ce matarsa ba ta son ya faɗi haka.
KU KARANTA: Aikin Hajji: Innalillahi Wa’inna Ilaihirraji’un (Hotuna)
Ya ce: “Idan ka taba matata, zan yi magana da Daddy (wato Allah ke nan) kuma za ka yi barci kuma ba za ka farka ba”.
Faston ya shawarci ma'aurata su kasance a shirye su sadaukar da ransu ga mai dakinsu.
Ya yi wannan magana ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Satumba a cikin wani sako a cocin na RCCG da ke Ebutte Meta, Legas.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng