Waiwayen Tarihi: Dubi jerin sunayen sarakunan da aka yi a jihar Kano tun zuwan mulkin turawa

Waiwayen Tarihi: Dubi jerin sunayen sarakunan da aka yi a jihar Kano tun zuwan mulkin turawa

Kafin zuwan mulkin Turawa, a 1903, masarautar daular Sakkwato ita ke mulkin jihar Kano da sauran kasashen Hausa, wannan na nufin Fulani kenan suke mulki, wadanda suka tumbuke mulkin Sarakunan Hausawa 'yan asalin yankin. Ya zuwa yanzu dai, Fulani ke mulkin kusan dukkanin gidajen sarauta a arewa.

Daga shekarar 1903 zuwa yanzu dai, anyi sarakunan Fulani guda tara wadanda suka fito daga tsatso daya, na Fulani, kuma dukkaninsu babu wanda masarautar Sakkwato ta dora, sai dai dorawar bature, ko dorawar masu mulki na zamani, wato 'yan siyasa.

Waiwayen Tarihi: Dubi jerin sunayen sarakunan da aka yi a jihar Kano tun zuwan mulkin turawa
Waiwayen Tarihi: Dubi jerin sunayen sarakunan da aka yi a jihar Kano tun zuwan mulkin turawa

* A shekarun 1909-1919 Sarki Muhammadu Abbas ne ya mulki Kano

* A shekarun 1919-1926 Sarki Usmanu na biyu ne a kan gadon Sarauta

* A shekarun 1926-1953 Sarki Abdullahi Bayero ne ke mulki, uba ga Ado Bayero

* A shekarun 1954-1963 Sarki Muhammadu Sanusi ke Sarauta, kaka ga sarki na yanzu

* A shekarar 1963 Sarki Muhammadu Inuwa ya karbi mulki, bayan tumbuke Sarki Sanusi

* A shekarun 1963-2014 Sarki Ado Bayero ne ke da Tagwayen Masu, kani ga hambararren Sarki Sanusi

* A shekarun 2014- Yanzu Sarki Sanusi Lamido Sanusi ke mulki, bayan rasuwar kawunsa Ado Bayero.

DUBA WANNAN: Jerin yawan ma'aikata a ma'aikatun Tarayya, daga kowacce jiha

An kafa jihar Kano ne dai a shekarar 999 Miladiyya watau kenan jihar tana da shekaru dubu daya da goma sha takwas da kafuwa.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng