Aljanna ma masoya da yawa: Musulmai da kiristoci sunyi gangamin yiwa Buhari addu'a a wannan jihar

Aljanna ma masoya da yawa: Musulmai da kiristoci sunyi gangamin yiwa Buhari addu'a a wannan jihar

Musulmai da kiristoci dake a jihar Gombe ta arewa maso gabashin Najeriya sun gudanar da bukukuwan sallah tare da wani dan kwarya-kwaryar gangami inda suka yi wa shugaba Muhammadu Buhari addu'ar samun lafiya a tare jim kadan bayan gama sallar idi.

Labarun da muka samu dai sun tabbatar mana da cewa shugabannin addinan biyu na musulunci da kiristanci da dama ne suka halarci gangamin yi wa shugaban addu'ar samun karin lafiya daga Allah.

Aljanna ma masoya da yawa: Musulmai da kiristoci sunyi gangamin yiwa Buhari addu'a a wannan jihar
Aljanna ma masoya da yawa: Musulmai da kiristoci sunyi gangamin yiwa Buhari addu'a a wannan jihar

Legit.ng haka zalika kuma ta samu labarin cewa taron ya kuma samu halartar manyan yan siyasa da sauran kungiyoyi daban daban dake a daukacin fadin jihar.

Wanda ya jagoranci taron Alhaji Abu Muazu Yariman wanda dan asalin karamar hukumar Kashere ne ya kuma gargadi su matasan kasar da su yi koyi da halaya na gari na shugaba Buhari inda kuma ya bayyana cewa abun da shugaban ya shimfida masu shi ne gaskiya da rikon amana da tausayin talakawa.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka yana mahaifar sa ta garin Daura dake a jihar Katsina inda yake gudanar da hutun sallah sa kamar yadda ya saba duk shekara.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng