Ko kunsan mutum nawa ne a Najeriya ke amfani da wayar salula?

Ko kunsan mutum nawa ne a Najeriya ke amfani da wayar salula?

- Adadin masu amfani da wayar salula ya kai mutum miliyan 145

- Adadin masu amfani da sadarwa ta wayar salula na raguwa

- Yawan masu amfani da wayar girke na samun ta gomashi

Hukumar "NCC" mai kula da kamfanunuwan sadarwar salula na kasa ta bayyana cewar adadin masu amfani da wayar salula domin sadarwa ya ragu zuwa mutum 149,249,150 daga 152,467,198. A wani bayanin hukumar da take fitarwa duk karshen Wata, NCC ta ce, an samu raguwar mutum 3,217,688 a watan afrilu sabanin mutum 151,999,197 da ke amfani da hanyar sadarwa ta salula.

Ko kunsan mutum nawa ne a Najeriya ke amfani da wayar salula?
wayar salula

Kamfanin Sadarwa na MTN ya rasa abokan hulda mutum 2,270,532 daga cikin mutum 60,391,959 da kamfanin ke da su a watan Mayu.

Kamfanin sadarwa na GLO ya samu raguwar abokan hulda mutum 58,727 daga cikin 37,328,827 da kamfanun ya ke da su a watan mayu.

Kamfanin sarwa na AIRTEL ya rasa abokan hulda 319,803 daga cikin jimillar mutum 34,656,605 da kamfanin ya ke da su a watan mayu.

Haka zalika kamfanin sadarwa na ETISALAT da yanzu ya koma 9MOBILE ya samu raguwar abokan hulda 576,120 daga cikin abokan hulda 19,045,686 da kamfanin ya ke da su a watan mayu.

DUBA WANNAN: Sallah: Aisha Buhari na taya 'yan Najeriya murnar babbar sallah

Sai dai hukumar ta 'NCC' ta ce adadin masu amfani da wayar girke ya karu, a saboda haka kamfanunuwan Sadarwa na VISAFONE da MULTILINKS basu yi asarar abokan hulda ba.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng