Farin ciki biyu ya riski musulmai
A aládar mallam Bahaushe, ranar Jumaá ta kasance rana mai matukar muhimmanci da girma, hakan yasa ake mata lakabi da Haji, babbar rana.
Sakamakon fadawar da ranar Sallar idin bana tayi a ranar Jumaá ya sanya musulamai da dama cikin farin ciki da doki.
Wani sahahararren malamin addinin musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil ya ce babu shakka "ai idi biyu ne suka hadu".
A cewarsa, idan aka ce yau karama ko babbar Sallah sun kama ranar Juma’a, toh ranar farin ciki biye ne suka riski musulmi.
Juma'a, ta kasance rana ce da musulmai daga wurare daban-daban kan taru duk mako a manyan masallatai don yin sallah raka biyu tare da sauraron huduba.
KU KARANTA KUMA: Nayi farin ciki da cewar gwamnonin kudu maso gabas sun gana da Kanu - Fayose
Saboda muhimmancin wannan rana ta Juma’a, wasu Musulman ba sa fita aiki, inda suke sadaukar da mafi rinjayen wunin ranar a masallaci.
Ranar tana da dumbin muhimmanci don kuwa Musulmai duk rintsi ba sa yarda su rasa sallar Juma'a uku a jere.
Sai gashi Sallah babba na bana ya fada a ranar Jum’a, don haka muna taya daukacin al’ummar musulmi fadin duniya murnar wannan rana.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng