Yanzu-Yanzu: Sojoji sun zagaye wani kauye a Bayelsa sakamakon kisan soja da sukayi
Wasu jami'ai a rundunar sojin Najeriya a yanzu haka sunyi wa wani kauye dake a cikin jihar Bayelsa kawanya a dalilin kisan dan uwan su da akayi tare da wani mutum a kauyen mai arzikin man fetur a jiya Laraba.
Ana dai zargin wasu yan bindiga dadi daga kauyen ne suka farma sojoji a dajen garin inda kuma har suka kashe daya daga cikin su a wajen wani dan tafki dake a wajen garin Letugbene a ranar Litinin din da ta gabata.
KU KARANTA: Yadda nike yaudarar yara in zan yi anfani da su - Wani mutum
Legit.ng ta samu labarin cewa yan bindiga dadin dai da yawan gaske ne suka farma sojojin kuma suka hau su da harbi ba kakkautawa. Labaran da muka samu kuma sun nuna mana cewa yayin da wani daga cikin matuka jirgin ruwan sojojin ya nemi rugawa ne sai yan bindigar suka harbe shi.
To tun bayan da labarin kisan na jami'in sojin ya kai ga mahunta a rundunar sai suka dauki mataki inda yanzu haka aka tura wasu zaratan sojin da dama su ka zagaye kauyen suna neman yan bindigar na nufin hukunta su.
Asali: Legit.ng