Labari cikin hotuna: Wasu ‘yan farauta sun bakonci gidan kaso a Bauchi
- Wasu ‘yan farauta sun kashe namomin daji ba bisa kaida ba a yankin jihar Bauchi
- An ci tara ‘yan farauta 3 naira 100,000 bayan da suka aikata ba daidai ba
- Hukumar kula da gandun daji ta kama wasu ‘yan farauta kuma an yanke masu watanni 5 a gidan yari
Hukumar kula da gandun daji a jihar Bauchi ta kama wasu ‘yan farauta 3 Munkailu Sani da Mai-Riga Ahmadu da kuma Umar Hussaini a ranar 19 ga watan Yuli a yankin Tungan-Kifi a gadun dajin Yankari da ke jihar Bauchi.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, ‘yan farautan da aka kama sun kasance daga Kashera wadanda ake zargi da kashe wasu naman daji biyu kafin a kama su.
KU KARANTA: Ina hukumar kare hakkin dabbobi ta Najeriya?
An ci tarar mutanen na kudi naira 100,000 ga kowani ko kuma su shafa watanni 5 a kurkuku. Amma ‘yan farautan sun kasa biyar wannan kudin sanadiyar aka kai su gidan kaso.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng