Ina hukumar kare hakkin dabbobi ta Najeriya?
Wani dan Najeriya ya yi kira ga hukumar kare hakin dabbobi ta Najeriya bisa yadda ake cin zarafin dabbobi a kasar.
Ya bayyana cewa ya kamata hokumar ta farka daga baccin da take yi, domin ta zagaya kasuwannin dabbobi domin ganin yadda ake daukar dabbobin cikin mota da sauransu.
Wannan kira na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta hada-hada tare da shirye-shiryen sallah layya a fadin kasar.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Okorocha ya hana adaidaita a Owerri
Shafin Rariya ce ta wallafa labarin kamar haka: “Ina Hukumar Kare Hakkin Dabbobi Ta Nijeriya?
“Hukumar dake kula da hakin dabbobi ta Nijeriya ya kamata ku tashi tsaye daga baccin da kuke yi, ku zagaya cikin kasuwanin da ake sayar da dabbobi. Domin kawo tsari na gaskiya wajen kulawa da yadda ake daukar dabbobi a mota da sauransu.”
Karin hotuna:
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng