Azal ta kai wani Kafinta ga satar Talo talo, ya gamu da hukunci mai tsanani
Wata karamar Kotu dake garin Kubwa na babban birnin tarayya Abuja ta yanke ma wani matashin Kafinta Rabiu ABdullahi hukuncin zaman gidan yari na watanni 4 kan satan Talo talo.
Alkalin kotun, Muhammed Marafa ya kama Rabiu da laifin yin kutse gidan da ba nasa ba, inda ya sace Talo talon a ranar 23 ga wata Agusta, kamar yadda kamfanin dillancin labaru ta ruwaito.
KU KARANTA: Makwabcin Sheikh Kabiru Gombe ya kai kararsa gaban kotu kan zarginsa da aikata wani lafi
Dansan mai shigar da kara, John Okpa ya bayyana ma kotu cewa Rabiu yayi kutse gidan wani mutumi ne mai suna Bello Marka Chikaroke wanda mazaunin garin Kubwa ne, inda yayi masa satar, kuma Bello ya kai kara caji ofis.
Dansandan yace sai da bincike yayi nisa ne aka gano talotalon daga hannun mutumin da ake zargi, wanda aka ce darajarta ta kai N25,000, hakan kuma ya saba ma sashi na 342 da 278 na kundin hukunta manyan laifuka.
A nasa bangaren, Rabiu ya amsa laifinsa, wanda hakan ya sanya alkalin kotun yanke masa daurin zaman gidan maza na tsawon watanni 4, inda yace ya san shi, tsohon mai laifi ne.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng