Kamfanin BUA ta buɗe katafariyar kamfanin Siminti a jihar Edo (Hotuna)
- Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara jihar Edo don kaddamar da aiki
- An bude kamfanin siminti a jihar mallakin kamfanin BUA
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci wata tawagar masu fada a ji zuwa jihar Edo inda suka kaddamar da fara aikin wani katafaren kamfanin siminti mallakin kamfanin BUA.
Wannan bikin kaddamarwan ya faru ne a ranar Talaat 29 ga watan Agusta a garin Okpella na jihar Edo, inda ake sa ran kamfanin simintin zai dinga samar da siminti tan miliyan 3, yayin da aka kashe ma kamfanin akalla dala miliyan 300.
KU KARANTA: Kwana 1000 na ɓarawo: An yi caraf da ɓarawon Ragon Sallah mai suna ‘Baletolli’ (Hotuna)
Cikin manyan da suka halarci taron sun hada da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Isiaka Rabiu, gwamnan jihar Edo da mataimakinsa da kuma gwamnan jihar Kano.
Sauran manyan baki a yayi taron suna hada da tsohon gwamnan jihar Edo, Adams Oshiomole, ministan harkokin cinikayya, ministan gona da sauran manyan yan kasuwa daga sassa daban daban na Najeriya.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng