Anyi ma wani dan Najeriya duka a Malaysia kan satar wayoyi
- An kama wani dan Najeriya yana satan wayoyi
- Wasu yan Najeriya ne suka zarge shi da sata
- Mai laifin yayi ikirarin cewa ya zo neman taimako ne domin biyan kudin gida, amman kofofi da ya gani bude ne yasa ya shiga sato wayoyi
Wasu yan Najeriya sunyi wa dan uwan su dukan tsiya a Malaysia bayan sun zarge shi da sace wayoyi da wasu muhimman kaya.
A wani bidiyo da wani Elder Igbinoghene ya yada a shafinsa na Facebook, an ga inda aka yiwa barawon tsirara.
Hannayen sa a daure lokacin da suke hukunta shi.
Barawon ya nemi a gafarce shi, ya bayyana cewa daga jihar Abia yake, ya zo neman taimakon kudin gida ne.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Kano ta bai wa kungiyar kwallon nakasassu kyautar mota
Da dai yaga cewa masu gidan sun fita sun bar kofofi bude, sai ya yanke shawarar sace musu wayoyi da wasu muhimman kaya.
Barawon yace shekaran sa na uku kenan a Malaysia sannan ya roki kungiyar mutanen da suka kama shi suka kuma yi barazanar kashe shi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng