Ku taimake mu kasar Iran na kera makaman kare-dangi suna shirin gamawa da mu - Kasar Isra'ila
Shugaba kuma firaministan kasar Isra'ila dake ci gaba da zama a tsakiyar laraba ya koka tare da neman taimakon majalisar dinkin duniya kan yadda yace kasar Iran na nan tana ta kera muggan makaman kare-dangi a kasashen Syria da Lebanon da nufin kai masu hari.
Benjamin Netanyahu dai shine yayi wannan kiran yayin dai yake ganawa da babban sakataren majalisar dinkin duniya mai suna Antonio Guterres a Jerusalem babban birnin kasar ta Isra'ila.
Legit.ng ta samu cewa Mista Netanyahu din dai ya kuma zargi kasar ta Iran da cewar tana maida kasashen wasu sansanonin kera makamai tare kuma da goyon bayan kungiyoyin yan ta'adda irin su Hezbollah da kuma gwamnatin Bashar Al-asad.
Duk da dai shugaban na yahudawan Isra'ila din bai yi wani cikakken bayani ba kan inda kasar ta Iran ke kera makaman a kasashen Syriya da Lebanon din amma dai ya ce wannan wani mataki ne da ba za su taba lamunta ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng