Rikita-Rikita: Kasar Koriya ta arewa ta sake harba makaman Nukiliya 3
Alamu dai na nuna cewa rikicin yan kin kasar Koriya bai ma kama hanyar karewa ba bayan da kasar nan ta Koriya ta Arewa ta sake harba manyan makaman Nukiliya har guda uku a jiya Juma'a duk kuwa da shiga tsakani da majalisar din kin duniya ta ke yi.
Kasar ta Koriya ta Kudu dai ita ce ta bayyana cewa makaman da makwafciyar ta ta harba ta harbo su ne daga yankin kasar na Gangwon kuma sai da suka ci zangon kilo mita 250 ko ka fin daga bisani su fada cikin ruwa.
Legit.ng ta samu dai cewa ana ci gaba da takun saka ne a tsakanin kasashen Amurka da ke da sansanin soji a kasar Koriya ta Kudu da kuma Koriya ta Arewa ne tun bayan da kasashen biyu suka fara wata matsananciyar gaba bayan gama yakin duniya na biyu.
Tuni dai majalisar dinkin duniya ta kakabawa kasar ta Koriya ta Arewa takunkumi amma hakan bai sa shugaban ta hatsabibi mai taurin kai ya janye kai hare-haren sa da kuma gwaje-gwajen makaman kasar sa masu linzami ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng