Daga karshe kungiyar Barcelona ta sayi magajin Neymar
Shahararriyar kungiyar kwallon kafar nan ta Barcelona dake taka leda a kasar Sipen ta amince da sayen dan matashin dan kwallon Borussia Dortmund din nan mai suna Ousmane Dembele kan zunzurutun kudin da suka kai fam miliyan 135.5.
Wannan ne ma dai ya sa dan kwallon ya zama na biyu mafi tsada a duniyar yan kwallo a halin yanzu da aka saya a bana, bayan wannan dan wasan Neymar da ya koma Paris St-Germain na kasar Faransa a kan fam miliyan 200 daga kungiyar ta Barcelona.
Legit.ng ta samu dai cewa kungiyar ta Barcelona za ta soma da biyan fam miliyan 96.8 kafin daga baya ta cika sauran kudin dan kwallon da har yanzu yake da shekara 20 kacal wanda kuma ya amince da yarjejeniyar shekara biyar a kungiyar.
Kawo yanzu dai dan wasan zai ziyarci kasar Sipen din a ranar Litinin domin likitocin Barcelona su duba lafiyarsa.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa kungiyar ta Dortmund ba ta amince da tayin da Barcelona ta fara yi wa dan kwallon a baya ba a watan Agusta, har ma ta dakatar da dan kwallon bayan da ya ki zuwa atisaye.
Asali: Legit.ng