An cafke wasu Yahoo boy ciki har da ‘yan Najeriya a Ghana (Hotuna)

An cafke wasu Yahoo boy ciki har da ‘yan Najeriya a Ghana (Hotuna)

- Hukumar ‘yan sandan kasar Ghana ta sanar cewa ta kama wasu ‘yan damfarar mutane a yanar gizo cikinsu har da ‘yan Najeriya

- Kimani mutane 26 ake zargi da aikata laifin damfarar

- ‘Yan sanda sun kwace kwamfyutoci da wayoyin salula da kuma wasu kayan aiki daga mutanen

Hukumar ‘yan sanda ta kasar Ghana tace ta kama wasu ‘yan damfarar mutane a yanar gizo wadanda aka fi sani da ‘Yahoo boys’ ciki har da 'yan Najeriya a ranar juma’a, 25 ga watan Agusta.

A cewar wasu rahotanni a shafuka ta yanar gizo na kasar Ghana, kimanin mutane 26 ciki har wasu ‘yan Najeriya daga cikinsu ake zargi da aikata laifuka na damfarar mutane a yanar gizo.

Wadanda ake tuhuma, wadanda shekarunsu suka kasance daga 19 zuwa 35 aka kama daga wani yanki na Ashale Botwe kusa da Madina a garin La-Nkwantanag / Madina na Greater Accra.

An cafke wasu yahoo boy ciki har da ‘yan Najeriya a Ghana (Hotuna)
'Yahoo boys masu damfarar mutane a yanar gizo

KU KARANTA: Uwa da 'yar ta da suka cillar da jariri sun sami tikitin zaman kurkuku a Katsina

'Yan sanda sun kwace kwamfyutoci 33, wayoyin salula 26 da kuma adadin sakonni daga masu tuhuma.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel