Labari mai daɗi: Buhari ya bada umarnin gina layin dogo Maiduguri zuwa Fatakwal

Labari mai daɗi: Buhari ya bada umarnin gina layin dogo Maiduguri zuwa Fatakwal

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a gina titin jirgin kasa daga jihar Kano zuwa garin Daura ta jihar Katsina, kamar yadda ministan sufuri Rotimi Amaechi ya bayyana.

Minista Amaechi ya bayyana haka ne yayin wani taron kara ma juna sani da aka yi a garin Abuja, wanda wata mata Osasu ta shirya don tattauna batutuwan tattalin arziki da inganta rayuwar talaka.

KU KARANTA: Buhari ya gana da shuwagabannin jam’iyyun Najeriya a fadar shugaban ƙasa (Hotuna)

Cikin titunan jirgin da Buhari ya amince a gina, akwai daga Fatakwal zuwa Maiduguri, Kano zuwa Maiduguri, Makurdi zuwa Jos, Gombe-Yobe zuwa Borno, sai kuma daga jihar Jigawa zuwa Nijar.

Labari mai daɗi: Buhari ya bada umarnin gina layin dogo Maiduguri zuwa Fatakwal
Jirgin kasa

Minista Amaechi ya koka kan yadda lamarin sufurin jirgin kasa ya tabarbare a Najeriya, sai dai yace a yanzu haka suna yin duk mai yiwuwa don ganin sun inganta harkar sufurin kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

“Kamfanin GE sunyi mana tayin zasu bamu tarragon jirgi guda 100, amma sai muka ga cewa hanyoyin irin jiragen mu ba zasu iya daukan sama da jirage 17 bakwai ba, don haka zamu kaddamar da taago 6 zuwa 10 a ranar 1 ga watan Oktoba da 2 ga wata.

“Muna sa ran daga watan Oktoba, kamfanin GE zata fara aiki daga Fatakwal zuwa Maiduguri.” Inji Amaechi

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel