Labarai cikin Hotuna: Shugabannin jam'iyyun APC da PDP sun kaiwa Shugaba Buhari ziyarar ban gajiya
Jawaban shugaba Muhammadu Buhari ga kusoshin jam'iyyun APC da PDP da suka kai masa ziyarar ban gajiya ta dawowa daga tafiyarsa
Shugaba Muhammadu Buhari ya fara jawabin nasa da nuna godiyar sa ta musamman akan gaba dayan tawagar da suka kai masa ziyara, sanadiyar samun dama da kuma lokaci da suka yi, na dauko hanya har zuwa garin Abuja domin kai masa wannan ziyara ta ban gajiya.
Yake cewa, "wannan ziyara tana nuna cewa kan Najeriya a hade yake, domin kuwa wannan ba taron nishadi bane kuma ba taron siyasa bane. Wannan alama ce ta hadin kai ta kasa. Har ila yau, wannan ziyara tana nuna irin munzalin da dimokuradiyya ta kai."
Ya kuma ce, tsarin dimokuradiyya na jam'iyyun siyasa shine tsarin gwamnati da aka gwada sosai kuma aka tabbatar wajen ciyar da kasa gaba. Harkokin adawa ba sa nufin rikici kuma ba sa nufin kiyayya ko cin amana. Dimokuradiyya tana bukatar 'yan adawa, amma kuma adawar ba ta nufin rabuwar kawunan al'umma.
"Na yi farin cikin ganin wannan taro naku duk da cewa akwai bambamce-bambamcen ra'ayoyi.Amma ina rokon ku da ku isar da sakon gaisuwa ta da kuma godiya ga maza da mata na cikin jihohin wajen irin addu'o'i da suka dukufa suna yi min."
KU KARANTA: Labarai cikin Hotuna: Ana yiwa Shugaba Buhari addu'o'i na musamman a jihar Kano
"Kuma ina shawartar gaba daya 'yan Najeriya da su cigaba da addu'o'in samun zaman lafiya a kasar nan domin duk abinda mutum ya sanya a gaba to kuwa sai da addu'a ake samun nasara."
A karshe ya ce, "ina kara gode muku kuma ina rokon Ubangiji d ya sanya albarka ga jamhuriyyar tarayyar Najeriya baki daya."
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng