Tashin hankali: Wani mutum ya hallaka ýar babban yayansa akan bashi N100

Tashin hankali: Wani mutum ya hallaka ýar babban yayansa akan bashi N100

Jama’an unguwar rimi dake garin Keffi na jihar Nassawar sun farka cikin firgici yayin da wata budurwa mai suna Amina Abdullahi ta rasu sakamakon jibgan ta da kawunta yayi mata.

Budurwa Amina Abdullahi wanda aka fi sani da suna Ummi, ta tafi wajen kawun nata, wanda kanin mahaifinta ne, Hamisu don karbar kudin da take bin shi bashi, N100.

KU KARANTA: Rundunar Ýansandan Najeriya ta daka wawa akan wasu masu garkuwa da mutane (Hotuna)

Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba 23 ga watan Agusta, a safiyar da ta je karbar kudin da take binsa bashi, inda daga nan ne fada ya kaure tsakaninsu har Hamisu ya jibge tad a karfin maza, kamar yadda jaridar Rariya ta ruwaito.

Tashin hankali: Wani mutum ya hallaka ýar babban yayansa akan bashi N100
Amina

Majiyar Legit.ng ta bayyana cewar yayin da Hamisu yake cikin dukan Amina ne sai ta yanke jiki ta fadi, inda aka yi aka yi ta tashi inaaa, ashe ta mutu, don koda aka garzaya da ita asibiti, ta riga ta rigamu gidan gaskiya.

Sai dai shima, Hamisu hankalinsa yafi na barawo tashi, inda shima a yanzu haka yana kwance a asibiti sakamakon shiga tashi hankali da yayi dangane da mutuwar Amina.

Tashin hankali: Wani mutum ya hallaka ýar babban yayansa akan bashi N100
Amina da saurayinta Nasir

Majiyar ta ruwaito cewa a bayan babbar Sallah ne ake sa ran Amina zata tayi auren ta na fari da angonta Nasiru Ibrahim.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng