Wani saurayi ya miƙa iyayensa ga ƙungiyar asiri don a yi masa tsafin kuɗi, amma…
Rundunar Yansandan jihar Anambra ta cika hannu da wani mutum Chukwuemeka Okafor mai shekaru 26 kan laifin mika iyayensa, kannensa biyu da abokanansa 5 don yin tsafin kudi.
Kwamishinan yansandan jihar Garba Umar ya shaida ma yan jarida cewa a ranar Alhamis 24 ga watan Agusta, inda yace mahaifin Chukwuemeka ya ba yaronsa N100,00, ashe bai san tsafi yaron nasa zai yi da shi ba.
KU KARANTA: Dansanda ya hallaka Maigidansa, shi kuma ya tunjuma cikin rijiya
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta rwuaito kwamishinan yana fadin yaron yayi ma babansa karyar zai yi kasuwanci ne, inda baban nasa ya aminta da shi, bayan amsan kudin sai ya garzaya wajen boka don a yi masa tsafin da zai iya kawar da babansa, kannensa biyu da abokanansa 5.
Daga karshe kwamishinan yace matashin na basu bayanan daya dace wajen bada sahihan bayanai, kuma za’a mika shi gaban kotu da an kammala bincike, kamar yadda majiyar Legit.ng ya ruwaito.
A nasa bangaren,matashin yace wani ne ya damfare shi N100,000 da sunan zai kai shi Dubai, “Daga nan ne na nemi taimakon wani attajirin abokina Zaki, wanda ya fada min sirrin dukiyarsa, kuma ya bani shawarar in shiga, shine nayi kokarin bada yan uwana” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng