Goron Juma’a: Kalli yadda ake tsaftace masallacin Annabi dake Madina

Goron Juma’a: Kalli yadda ake tsaftace masallacin Annabi dake Madina

- Masallacin Annabi shine masallaci na biyu mafi daraja a Duniya

- Akwai ma'aikata kimanin 3,200 dake aikin tsaftace masallacin

Sakamakon yawan mahajjata dake kai ziyara masallacin Annabi dake birnin Madina, kasar Saudiyya, gami da yawan karunwa jama’a dake zuwa yin Ibadah a masallacin, hakan ya sabbaba tsaftace masallacin akai akai.

Sanannen abu ne a Musulunci cewar masallacin Annabi ne na biyu wajen daraja a masallatan Duniya gaba daya, bugu da kari a cikin masallacin ne kabarin Annabi yake.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Gwamnan jihar Zamfara ya musanta muradinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa

Goron Juma’a: Kalli yadda ake tsaftace masallacin Annabi dake Madina
Aikin tsaftace masallaci

Kaakakin hukumar kula da tsaftar masallacin dake karkashin fadar Sarkin Saudiyya, Hatab yace “Muna raba aikin sharewa da wanke masallacin kashi 4 ne, sa’annan akwai kimanin ma’akata 3,200 da suke yin wannan muhimmin aiki.”

Ga bidiyon nan:

Legit.ng ta ruwaito Kaakakin yana bayyana cewa aikin tsaftace masallacin ya hada da wanke ginshikan cikin masallacin, silip, tandaryar kasar masallacin, hasumiyarsa da kuma na’aurar tafiya da mutane. Haka zalika akwai masu wanke wajen nan da tantabaru ke taruwa, da kuma masu wanke bayi.

Goron Juma’a: Kalli yadda ake tsaftace masallacin Annabi dake Madina
Aikin tsaftace masallacin Annabi

“Da zarar baki sun sha ruwa a masallacin da watan Ramadana, muna da tsarin kwashe abincin da suka rage, inda muka zubar dasu, ba tare da bata lokaci ba cikin mintun 40 mun kallama aikin.” inji shi.

Goron Juma’a: Kalli yadda ake tsaftace masallacin Annabi dake Madina
Aikin tsaftace masallacin Makkah

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wani Yaron Fasto ya koma Musulunci:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng