Miji na sullutu ne, ba ya iya tabuka mun komai - wata mata ta shaidawa kotu

Miji na sullutu ne, ba ya iya tabuka mun komai - wata mata ta shaidawa kotu

Wata mata mai suna Amina Suleiman ta bukaci wata kotu dake zama a jihar kwara a karamar hukumar Iliri da ta lalata auren su da mijin ta saboda a cewar ta mijin sullutu ne ba ya iya sai mata ko da dan kamfai ne.

Da take bayar da ba'asi a gaban alkalin kotun, Amina Sulaiman ta shaidawa kotun cewa mijin nata sam baya kula da ita ko kadan ita da ya'yan su don kuwa ita ke daukar dawainiyar hakan.

Miji na sullutu ne, ba ya iya tabuka mun komai - wata mata ta shaidawa kotu
Miji na sullutu ne, ba ya iya tabuka mun komai - wata mata ta shaidawa kotu

Legit.ng ta samu daga majiyar mu cewa Amina tace: "Allah ya albarkaci auren mu da 'ya'ya har biyu amma mijina bai san cin su ba balle shan su. Duk ni ke yin komai kuma yanzu na gaji."

Ta ci gaba da cewa: "Mijin nawa kuma uban 'ya'yan har ila yau ba ruwan sa da kudin makarantar yaran to balle ma ya bani kudin da zan siya kaya ko wasu sauran bukatu na."

Daga karshe dai alkalin kotun ya yanke shawarar rusa auren saboda a cewar sa dukkanin ma'auratan sun gaji da junan su don haka zama tare a gare su bai da wani anfani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel