An kama wani dan shekara 38, yana satar wanduna daga dakin ajiye kaya na asibiti a matsayin kyauta ga budurwarsa
- An kama wani mutumi mai shekaru 38 a Thailand yana satan wanduna daga asibiti
- Barawon wandon yayi ikirarin cewa ya aikata hakan ne saboda budurwar shi
- An rahoto cewa wandunan mallakar dangin wani mai jinya ne a asibitin Udon Thani
An kama wani mai shekaru 38, a yayinda yake satar wanduna da aka shanya a wajen asibitin Udon Thani.
Masu gadi ne suka cafke shi a asibitin a yayinda ya kwashe wandunan matar daga inda aka shanya a asibitin ba tare da kunya ba.
An rahoto cewa ya riga ya saci wanduna hudu, masu kaloli daban daban a lokacin da aka kama shi.
Da yake kare kansa, Prasertkaew mai laifin yace yayi hakan ne saboda budurwar shi, wacce take sanya wanduna masu ramuka.
KU KARANTA KUMA: Bikin babban Sallah: Jihar Lagas ta yi odar tireloli 70 na buhuhunan shinkafa
Prasertkaew ya bayyana yanda ya rasa aikinsa a wassu yan watanni da suka gabata, hakan ne yasa ya kasa siya wa budurwar tashi wanduna.
Daga karshe anyi kunnen uwar shegu da rokonsa inda aka chaje shi da laifin sata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng