Wata mata ta nemi kashe aurenta a kan rikicin mijinta

Wata mata ta nemi kashe aurenta a kan rikicin mijinta

Wata matar aure, Asmau Abdullahi, ta roki kotun sharia ta Minna ta raba aurenta da mijinta saboda yawan duka da kuma zage-zage da take sha a gun mijin nata.

Asmau ta shaidawa kotu cewa mijinta, Ibrahim Abdullahi, ya saba yi mata duka ne ba a kowani dalili ba.

"Mijina ya na zagi na a kowani lokaci kuma ya na kira na sunaye kamar mahaukaciya ,mace marar hankali da kuma sauransu.

"Yana duka na a kowani lokaci,kuma yana tilasta ni jan ruwa daga rijiya a cikin sa'o'i na dare.

"Ba ya nuna mini ƙauna, kuma shi ya sa nake so in kawo karshen wannan aure," in ji ta.

Wata mata ta nemi kashe aurenta a kan rikicin mijinta
Wata mata ta nemi kashe aurenta a kan rikicin mijinta

KU KARANTA KUMA: Yan ta’addan Boko Haram 68 sun mika wuya a jihar Borno

Amma, Ibrahim ya ki amincewa da zargin matarsa, ya kuma ce ya kasance mijini mai kirki.

Ya ci gaba da cewa har yanzu yana ƙaunar matarsa ​​kuma ba zai so su rabu ba.

Alkalin, Malam Ahmed Bima, ya shawarci ma'aurata su ba da damar zaman lafiya da warware matsalolin su, kamar yadda aure ya bukaci cikakken hakuri da fahimta.

Ya dakatar da shari'ar har zuwa ranar 11 ga watan Satumba, don ba da dama ga bangarorin biyu su magance bambancin dake tsakanin su. (NAN)

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng