Miji na ya dage sai mun cigaba da zaman zina bayan ya sake ni saki 3 - Mata ta shaidawa kotu
Wata mata mai suna Fatima Larai Ndako ta shigar da kara a wata kotu dake zama a Gwagwalada inda ta shaidawa kotun cewa mijin ta mai suna Mustapha I Sulaiman ya dage sai sun ci gaba da zama bayan yayi mata saki uku ringis.
Ita dai Ndako ta shigar da karar ne a kotun inda kuma ta roki alkalin da ya raba auren su mai shekara biyar tun da dai minjin nata ya sake ta har sau uku kuma zaman na su ya haramta.
Legit.ng ta samu cewa alkalin kotun mai suna Musa Umar Angulu ya ce duk da yake cewa musulunci ya bayar da dama ga miji ya saki matar sa idan hakan ya zama dole, to fa dole ne ya ci gaba da bata hakkin ta har sai ta gama idda.
Daga nan ne dai sai kotun ta yanke hukuncin lalata auren bayan da aka bukaci su sasanta kan su a wajen kotun har sau uku. Shima dai mijin yace yaji dadin hukuncin.
Asali: Legit.ng