Dandalin Kannywood: Ban isa aure ba, duka-duka shekaru na 23 - Rahma Sadau
Shahararriyar jarumar nan ta wasannin fina finan Hausa wadda kuma yanzu haka ke a matsayin korarriya a masana'antar Kannywood watau Rahma Sadau ta bayyana cewa ita yanzu bata da saurayi don kuwa duka-duka shekarar ta 23 a duniya.
Jarumar ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata fira da tayi da manema labarai a game da rayuwar ta a dandamalin Kannywood.
Legit.ng ta samu a firar ta ta ta jarumar ta kuma bayyana cewar ba za ta taba fidda tsiraicin ta ba duk kuwa da cewar yanzu ta rungumi sana'ar yin fina-finan kudancin kasar nan gadan-gadan.
Haka ma dai jarumar yan asalin garin Kaduna ta kuma dauki dogon lokaci tana sharhi da kuma nuna rashin jin dadin ta game da yadda tace al'ummar hausawa nayi wa harkar tasu mummunar fassara inda ta kara jaddada cewa shifa fim, fim ne ba wai da gaske bane.
Tun farko dai, jarumar ta godewa dukkan masoyan da suka fito kwarsu da kwarkwata domin taimaka mata.
Asali: Legit.ng