Rana ta haska baiwa: Labarin wata zaƙaƙurar yarinya yar jihar Zamfara data kafa tarihi

Rana ta haska baiwa: Labarin wata zaƙaƙurar yarinya yar jihar Zamfara data kafa tarihi

- Cibiyar samar da cigaba ta kasar Birtaniya, DFID ta kirkiro wani tsarin ilimantar da yara mata

- An samu wata yarinya yar Zamfara da tayi fice a fannin lissafi da karatun Turanci

A kokarinta na inganta ilimin mata a yankin Arewa, cibiyar samar da cigaba da kasar Ingila, DFID ta fito da wani tsarin koyar ma mata dake kauyuka lissafi da harshen turanci, mai suna ‘RANA’.

Jaridar Inside Nigeria ta ci karo da wata yarinya mai suna Fatima, wanda tayi fice a wannan shiri tare da nuna kwazo, sa’anann itace mace ta farko data fara yin karatun Boko a danginta, bugu da kari tana da burin zama likita.

KU KARANTA: Hukumar kwastam ta ƙwace wani sunduƙi cike da kayan Sojoji da ya shigo daga ƙasar Sin

Rana ta haska baiwa: Labarin wata zaƙaƙurar yarinya yar jihar Zamfara data kafa tarihi
Fatima

Tsarin ilimi na RANA ya hada har da karatun addini, musamman karatun Qur’ani, a yanzu haka kimanin kashi 28 na dalibai mata dake tsarin sun nuna kwarewa wajen yin lissafi da magana da harshen Turanci

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mahaifin Fatima, Malam Dayyabu manomi ne, yayin da mahaifiyarta yar fura fura ce, amma duk da talaucinsu basu hana yarsu zuwa makaranta ba. Malam Dayyabu yace yana alfahari da yarinyar nan, kuma zai bata dukkanin gudunmuwar da take bukata.

Rana ta haska baiwa: Labarin wata zaƙaƙurar yarinya yar jihar Zamfara data kafa tarihi
Fatima a makaranta

A kullum Fatima ta kan fada ma mahaifinta burinta shine ta zama likita, inda a duk lokacin data dawo daga makaranta, sai ta kawo masa littafin ta don yin bitar abin da aka karantar da ita.

Rana ta haska baiwa: Labarin wata zaƙaƙurar yarinya yar jihar Zamfara data kafa tarihi
Fatima da mahaifiyarta

Bugu da kari, kokarin da Fatima keyi a makaranta ya sa tana burge makwabtan su, tare da jama’n garinsu, hakan ta sanya wasu lokuta suke rage mata hanya, sakamakon makarantar da take zuwa akwai nisa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Wani shugaba yafi a cikin wadannan?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng