Dabaru guda 3 da gwamnati zata bi don fatattakar ɓerayen da suka mamaye ofishin Buhari

Dabaru guda 3 da gwamnati zata bi don fatattakar ɓerayen da suka mamaye ofishin Buhari

A ranar Talata 22 ga watan Agusta ne fadar shugaban kasa ta bayyana ma duniya cewar beraye sun shiga ofishin shugaban kasa dake fadar, inda suka yi kaca kaca da kayayyakin ofishin.

Kaakakin shugaban kasa Garba Shehu ne ya bayyana haka ga manema labaru a wata hira da yayi da BBC Hausa, inda yace sakamakon kwashe sama da kwanaki 100 da shugaban kasa yayi a birnin Landan yana jinya, hakan ne ya basu beraye dama shiga ofishin.

KU KARANTA: Harin tsanar baƙi: Matasa a Ghana sun afka ma ýan Najeriya mazauna ƙasar, sun hallaka mutum 5

Bugu da kari, duba da cewa ofishin na shugaban kasa ba kasafai ake shigarsa, don haka ba’a Ankara da matsalar ba har sai da shugaban kasar ya dawo gida Najeriya.

Dabaru guda 3 da gwamnati zata bi don fatattakar ɓerayen da suka mamaye ofishin Buhari
Beraye a Ofishin Buhari

Sai dai Legit.ng ta binciko wasu hanyoyi ko dabaru da za’a iya amfani dasu wajen magance matsalar beraye a ofishin shugaban kasa, da sauran wuraren zama.

1- Kyanwa/Mage/Kuliya

Sanannen abu ne cewa mage da bera basa ga maciji, wannan ne ya sa tun a zamanin dauri ake amfani da mage wajen fatattakar beraye daga gida ko daki.

Don haka gwamnati na iya ajiye mage a ofishin shugaban kasa, musamman yadda aka san akwai kyakkyawan alaka tsakanin Mage da Mutum, don haka ba zata cutar da shugaban kasa ba, kuma zata yi maganin berayen.

2- Tarko

Idan bera ya gagara, akan yi amfani da tarko don kama shi, hakan kuma na da tabbacin samun nasara tun da ko a kauyuka abinda jama’a ke amfani da shi kenan wajen kama gafiya don yin farfesun ta.

Shima tarkon za’a iya samun irin na zamani mai ban sha’awa, a sanya shi a ofishin shugaban kasa, tabbas ko ba jima ko ba dade zata kama berayen da suka addabi ofishin.

3- Maganin Bera

Hanya na uku da gwamnatin Najeriya zata iya bi don maganin bera shine amfani da maganin bera, wanda zai hallaka beran da ire irensa. Sau dayawa akan yi amfani da maganin ne tare da kifi ko wani nau’in abinci dab era ke so, daya ci sai ya mutu.

Amma a yanzu cigaba ya sa an samu maganin bera wanda ko sun ci, ko basu ci ba, zai hallaka su, muddin sun shaki warins. Shima wannan wani hanya ne da fadar shugaban kasa zata iya bi wajen ganin anyi maganin berayen dake ofishin shugaban kasa.

Fatan mu a nan shine, Allah yasa berayen nan basu cinye wasu takardu masu muhimmanci ga cigaban kasa ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng