Ban yi magana da Ali Modu ba tun bayan hukuncin kotu - Makarfi

Ban yi magana da Ali Modu ba tun bayan hukuncin kotu - Makarfi

- Makarfi ya bayyana cewar ba alhakin sa ba ne ya yi magana ko tuntubar Ali Modu ba

- Makarfi ya yi Karin haske a kan jita jitar yana son yin takarar shugabancin kasa

- Arewacin Nigeria ne zai fitar da dan takarar shugabancin kasa

Shugaban riko na jam'iyyar PDP, Sanata Ahmad Makarfi, a wata tattaunawa da a ka yi da shi ya bayyana cewar tun bayan hukuncin Kotun da ya tabbatar da shi a matsayin shugaban jam'iyyar PDP ba su yi magana da tsohon shugaban rikon jam'iyyar ba, Ali Modu sheriff.

Makarfi ya bayyana cewar ba alhakin sa ba ne ya yi magana ko tuntubar Ali Modu ba domin jam'iyya ta kafa kwamiti na musamman domin sasanta ya'yan jam'iyyar sannan ya karyata maganar cewa sun kori magoya bayan Ali Modu daga wurin da taron gangami da jam'iyyar ta gudanar.

Da ya ke amsa tambaya a kan wane kokari ya ke yi domin ganin Ali Modu din bai bar PDP ba, makarfi ya ce "wannan magana ce da bata shafeni ba, ganin damar sa ne ya zauna ko ya bar jam'iyyar".

Ban yi magana da Sherriff ba tun bayan jojin kotun koli - Makarfi
Ban yi magana da Sherriff ba tun bayan jojin kotun koli - Makarfi

Makarfi ya yi Karin haske a kan jita jitar yana son yin takarar shugabancin kasa, "aikin da ya ke gabana na dawo da kima da martabar PDP ne, bani da niyyar shiga takara ko wacce iri ce", ya Kara da cewa idan lokaci yayi jam'iyyar zata fitar da dan takarar shugabancin kasa ne daga arewa.

DUBA WANNAN: Arewa daya ce; Ba wani yankin tsakiya – Kwande

PDP dai ta lashi takobin kwace mulki daga hannun APC a zabukan 2019, amma ga dukkan alamu, talakawa na kule da makudan kudade da aka sace a lokacin mulkin su 1999-2015. Masu dai nemi afuwar talakawa ba ila yanzu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng