Wani magidanci ya yi ido hudu da matarsa tare da wani a gidan shakatawa

Wani magidanci ya yi ido hudu da matarsa tare da wani a gidan shakatawa

Wata kotu dake garin Mapo na jihar Oyo ta raba auren wasu maáurata biyu Kabir Bakare da mai dakinsa Fumilola sakamakon zargin yin lalata da wasu mazan banza a waje.

Kabir Bakare ya sanar da kotun cewa matarsa na bin maza duk kuwa da cewan babu abunda ya gaza yi mata a matsayin shin a mijinta.

A cewarsa makwabta da abokan arziki sun sha kokarin nusar da shi halin da matar tasa sannan shi kuma ya sami tabbacin hakan da ya kamata dumu-dumu da wani daga cikin samarin ta.

Fumilola ba tace komai akan zargin da ake yi mata ba sai dai ta sanar da kotu cewa mijinta ya hana ta ganin danta.

Ta kuma roki alfarmar kotun da a bata izinin kwashe sauran kayan ta dake gidan Kabiru Bakare.

KU KARANTA KUMA: Don murnar dawowar Buhari, wadannan yan Najeriyan sunyi liyafa da naman akuya (hotuna)

Alkalin kotun Ademola Odunade bayan sauraron su ya raba auren saboda rashin soyyaya dake tsakanin ma’auratan sannan ya dankawa Kabir nauyin kula da dan nasu wanda shekaransa biyu kenan a duniya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel