Subhanallah! An zargi kishiya da kisan amarya a ranar daurin ta a Sokoto

Subhanallah! An zargi kishiya da kisan amarya a ranar daurin ta a Sokoto

Labarin da muka samu daga majiyoyi da dama na nuni da cewa Allah ya karbi ran wata amarya a garin Sokoto dake a arewa maso yammacin Najeriya a ranar daurin auren ta.

Kamar dai yadda rahotannin na mu suka nuna amaryar ta fadi ne kasa kawai ta mutu a sakamakon wani matsanancin ciwon kai da ta ce tana fama da shi jim kadan bayan ai gama daurin aure kuma ana shirin tafiya kaita dakin ta.

Subhanallah! An zargi kishiya da kisan amarya a ranar daurin ta a Sokoto
Subhanallah! An zargi kishiya da kisan amarya a ranar daurin ta a Sokoto

Legit.ng ta samu cewa bayan an kammala daurin aure da safe, lokacin da ango ya turo motoci domin a daukar masa ita sai amarya ta bayyana masu cewa kanta na matsanancin ciwo sosai don haka a dakata.

Kamar ba za a dakata ba, amma ganin yadda ta matsa har da kuka akan ciwon kan nata sai aka bukaci a jira zuwa mintuna talatin a ga ya za a yi ko ciwon kan zai sassauta amma sai Allah ya karbi abun sa.

Tuni dai mutane suka fara zargin kishiyar da kisan inda suka ce daman can uwar gidan bata so auren ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel