Dandalin Kannywood: Allah bai wajabta mani in yi aure ba - Inji Shehiyar malama Ummee Zee-Zee

Dandalin Kannywood: Allah bai wajabta mani in yi aure ba - Inji Shehiyar malama Ummee Zee-Zee

Shahararriyar tsohuwar jaruma a wasan fina-finan Hausa mai suna Ummee Zee-Zee ta fito ta fadawa duniya cewa Allah fa bai wajabta aure ba akan dukkan mutane don haka a shafa mata lafiya.

Kamar yadda muka samu daga majiyar mu, jarumar ya yi wannan kalamin ne kusan a matsayin raddi ga al'umma mutane da ke ta caccakar ta da kuma ire-iren ta da cewa sun ki suyi aure duk kuwa da cewa shekarun su sun ja.

Dandalin Kannywood: Allah bai wajabta mani in yi aure ba - Inji Shehiyar malama Ummee Zee-Zee
Dandalin Kannywood: Allah bai wajabta mani in yi aure ba - Inji Shehiyar malama Ummee Zee-Zee
Asali: UGC

Legit.ng dai ta samu cewa a kwanan baya ma dai wata tsohuwar jarumar a masana'antar fina-finan Hausa Fati Muhammad ta fito ta bayyana babbar nadamar ta a rayuwa a matsayin auren dan fim Sani Musa Mai iska da tayi a shekarun baya.

Su dai jaruman fina-finan Hausa musamman ma dai mata a cikin su na fuskantar matukar matsin lamba daga al'ummar Hausa inda kuma a lokuta da dama akan zarge su da bata tarbiyyar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng