Dan shekara 40 ya zakke ma ƙaramar yarinya ýar shekara 6, ya gamu da hukunci mai tsada

Dan shekara 40 ya zakke ma ƙaramar yarinya ýar shekara 6, ya gamu da hukunci mai tsada

A gurfanar da wani mutumi Ademola Ogunlana gaban kuliya manta sabo kan tuhumarsa da laifin yi ma wata karamar yarinya yar shekara 6 fyade a jihar Legas.

An gurfanar da Ademola mai shekaru 40 ne kan zargin zakke ma yarinyar ne, inji dansanda mai kara, Sajan Anthonia Osayande, wanda yace lamarin ya auku ne a ranar 26 ga watan Yuli da misalin karfe 4 na yamma.

KU KARANTA:Babbar Sallah: Don gudun kada ta wuce ta bar wawa da bashi, kula da waɗannan abubuwa 3

Dansanda mai kara yace mutumin ya samu daman zakke ma yarinyar ne sakamakon suna zaman gida daya, kuma ya afka mata ne a lokacin da iyayenta suka fita zuwa aiki, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Dan shekara 40 ya zakke ma ƙaramar yarinya ýar shekara 6, ya gamu da hukunci mai tsada
wata Kotu

Majiyar Legit.ng ta tabbatar da cewar mutumin ya soka hannunsa a gaban yarinyar ne, sa’annan yarinyar ta kai kararsa ga mahaifiyarta, a haka ne aka kama shi.

Sai dai mutumin ya musanta zargin da ake yi masa, hakan ta sanya alkali mai shari’a Ipaye Nwachukwu bada belinsa akan kudi naira dubu N500,000, da mutane 2 da zasu tsaya masa.

Daga nan sai mai shari’a ta dage sauraron karar zuwa ranar 19 ga watan Oktoba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng