Babbar Sallah: Don gudun kada ta wuce ta bar wawa da bashi, kula da waɗannan abubuwa 3

Babbar Sallah: Don gudun kada ta wuce ta bar wawa da bashi, kula da waɗannan abubuwa 3

Babbar Sallah ke karatowa, don har mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bada umarnin a fara neman sabon watan Zul Hajji daga ranar 22 ga watan Agusta.

Don haka Legit.ng ta kawo muku wasu hanyoyin guje ma shiga matsalar bashi, wanda Hausawa ke ce ma ‘Sallah ta wuce, ta bar wawa da bashi.’

Layya

An hori Musulmai da kada su jefa kansu cikin matsalar bashi domin yin layya, kamar yadda wani shehin Malami daga jami’ar Ilori Badmas Yusuf ya bayyana.

KU KARANTA: Muhimman batutuwa 7 da Buhari yayi a yayin jawabin da yayi ma ýan Najeriya a yau

Malamin ya gargadi Musulmai da su guje cin bashi don yin layya, saboda Allah ba zai kama su da abinda yafi karfinsu, kuma Allah baya wajabta ma mutum yin layya, muddin karfinsa bai kai ba.

Babbar Sallah: Don gudun kada ta wuce ta bar wawa da bashi, kula da waɗannan abubuwa 3
Raguna

Almubazzaranci

Sanannen abu ne addinin Musulunci ya haramta ma Musulmai yin almubazzaranci, kamar yadda Allah ya fadi a Qur’ani. Don haka ake gargadin jama’a Musulmai da kada su yarda shedna ya jefa su cikin halin almubazzaranci da kudi, ko abinci da sunan bikin Sallah.

Dinkin Sallah

Dinkin sababbin kaya a bikin Sallah abu ne muhimmi ga Musulmai a yayin bukukuwan Sallah, don kuwa Annabi Muhammadu SAW ma yayi umarni da Musulma su sanya sabbin kaya ga masu hali a ranar Sallah, ko kuma mutum ya sanya kayan da suka fi kyau a cikin kayansa.

Sai dai wasu mutane su ka wuce gona da iri wajen yin hakan, inda sai suci bashi don yin dinkin Sallah, kuma su hana teloli masu hakki kudadensu.

Da fatan jama’a zasu guje ma shiga wata matsala a yayin wannan bikin Sallah mai karatowa, Allah ya kai mu da rai da lafiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel