Hatsari a teku: Kwalekwale ya kifa da mutane a Legas, mutum 12 sun cika
- Kwale kwale a Legas ya kifa da wasu mutane a tafkin Legas
- An bayyana diban fasinjoji fiye da kima ne ya janyo wannan hatsari
Wani hatsarin teku ya rutsa da wasu matafiya a cikin kwalekwale yayin da kwale kwalen ya kifa dasu, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar mutane 12, inji rahoton Premium Times.
Shugaban hukumar kula da ruwan Legas, Abisola Kamson ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta danganta shi da diban fasinja fiye da kima, tare da cewa tashar daga inda kwalekwalen ta tashi haramtacciya ce.
KU KARANTA: Dawowar Buhari: Ana tsammanin zai fatattaki ‘Kurayen’ dake zagaye da shi
Shugaban hukumar ta shaida ma majiyar Legit.ng cewa an ceto mutum hudu daga cikin wadanda hatsarin ya rutsa dasu, kuma tuni suna samun kulawa a asibiti, yayin da ana cigaba da neman sauran a cikin ruwa.
Sai dai shugaban hukumar ta janyo hankalin hukuma kula da hanyoyin ruwa ta kasa, NIWA, data mutunta hukuncin kotu data baiwa jihar Legas daman kulawa da hanyoyin cikin ruwanta, wanda tace hakan en zai baiwa gwamnatin daman gudanar da ayyukanta yadda ya dace.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng