Chamfi da Tsafi: Charaf an sake kama matsafa da sassan jikin mutane

Chamfi da Tsafi: Charaf an sake kama matsafa da sassan jikin mutane

A Najeriya, da yawa daga jama'arta sun amanna da chamfi, kan cewa wai wani bari na jikin mutum ko dabba zai iya zama kudi idan aka fadi wasu kalmomi. Shirme da jahilci yayi mana kauci.

A jiya ne hukumar ‘yan sandan Okporo a Port Harcourt suka cafke wani matashi mai suna Ifeanyi Chukwu wanda aka kama shi da zargin sace yarinya ‘yar shekara 8.

Wasu mutanen suna satar yara ne tare da cire wasu sassa na jikinsu da niyyar siyarwa ko anfani da su ta wata hanyar da zata zame musu kudi.

Chamfi da Tsafi: Charaf an sake kama matsafa da sassan jikin mutane
Chamfi da Tsafi: Charaf an sake kama matsafa da sassan jikin mutane

Yarinyar mai suna Chikamso Victory, an tsince ta a mace ne an yanke wassu sassa na jikin ta da kulle su a bakar leda.

Wani dan unguwar da ya lura da alamomin rashin gaskiya a tattare da yaron sai ya tare shi, bayan ya mishi tambayoyi sai yaron ya kama mutumin da kokawa, An cafke yaron a hanyarsa ta zuwa yar da gawar yarinyar.

KU DUBA: PDP Ta Lashe Zaben Dan Majalisa A Gombe

A take aka chafke yaron da mika shi zuwa hannun 'yan sanda, bayan tuhumar da ‘yan sanda suka masa ne ya fadi abubuwan da ya aikata da inda ya boye sassan jikin yarinyar.

‘Yan sanda sun dauki gawar yarinyar da sassan jikinta an kai dakin da ake ajiye gawawwaki, shi kuma Ifeanyi Chukwu an tsare shi don cigaba da bincike.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel