Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

-Rundunar yan sandan jihar Bayelsa sun cafke yaro dan shekara 10 da ke fashi da sata

-Yaron mai suna Victor yace kawunsa ne ya koya masa sata da fashi bayan rasuwar mahaifinsa

-Victor yana neman gafaran mutane kuma yana rokon gwamnati ta kula dashi domin baya so ya koma muguwar sana'ar ta sata

Yaro dan sheka 10 mai suna Victor Tarekedomoni ya labarta yadda ya tsinci kansa a muguwar aikin fashi da makami, yayi bayanin ne a lkoacin da jami'an rundunar yan sanda na jihar Bayelsa suke masa tambayoyi.

Victor dai ya kware a satan wayar salula a tashoshin mota da kuma haura katanga domin shiga cikin gidajen mutane har ma da matse jikinsa tsakanin karafunan kofa ko taga domin shigewa gidajen mutanen inda yake satan kayan alatu kaman yan kunne, kudade, wayoyin salula da ma wasu abubuwa.

Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami
Dan shekara 10 ya labarta yadda ya zama gawurtaccen dan fashi da makami

Victor ya taimaka ma wasu yan fashin wajen sata sau da yawa kafin yan sanda su cafke shi.

DUBA WANNAN: Hukumar 'Yansanda ta bankado matsafa da ake yankan kan yara

Karamin yaron dai ya shaida wa jami'an yan sanda cewa kawun sa ne ya fara koya masa sata bayan rasuwar mahaifinsa.

Yace, "Mahaifina ya rasu tun ina dan karami sosai, bayan haka sai na koma wajen kawu na da zama inda ya koya min yadda zanyi sata da fashi. Kawu na ya tura ni wurare daban-daban a unguwar mu domin inyi sata.

"Akwai wani lokaci da ya aike ni wani ofis domin in sato talabijin da komfuta, kuma na aikata hakan. A lokacin ina zuwa makarantar frimari ta Universal Basic Primary School a garin Ovum, na dena zuwa makaranta a aji 4 bayan kawu na yaje wani sata amma daga bayan yan sanda suka zo gida neman sa amma ya tsere, bayan tserewarsa sai na dena zuwa makaranta na shiga kungiyar yan fashi.

"Idan munje fashi, sauran manyan suna dora ni a katanga, ni kuma sai in shiga gidan in sato abubuwan alatu, daga baya sai su bani N1000 ko N1,500 wanda zan ci abinci dashi.

"Ina neman gafaran mutane da kuma gwamnatin jihar Bayelsa, ina son in zama dan kasa na gari. Na fara fashi ne saboda ban samu kulawa daga iyaye na ba, sunnan kungiyar fashin mu Greenlander cult group. sunayen sauran yan kungiyan mu sun hada da Junior, Finefine, Daddy Boy, Godspower, Kempede and Goodtimes."

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng